2 Da na duba, ga farin doki, mahayinsa kuma yana da baka, aka ba shi kambi, ya kuwa fita yana mai nasara, domin ya ƙara cin nasara.
3 Da ya ɓamɓare hatimi na biyu, na ji rayayyiyar halittar nan ta biyu ta ce, “Zo.”
4 Sai wani jan doki ya fito, aka kuma ba mahayinsa izini yă ɗauke salama daga duniya, don mutane su kashe juna, aka kuma ba shi babban takobi.
5 Da ya ɓamɓare hatimi na uku, na ji rayayyiyar halittar nan ta uku ta ce, “Zo.” Da na duba, ga baƙin doki, mahayinsa kuwa da mizani a hannunsa.
6 Sai na ji kamar wata murya a tsakiyar rayayyun halittar nan huɗu tana cewa, “Mudun alkama dinari guda, mudu uku na sha'ir dinari guda, sai dai kada ka ɓāta mai da kuma ruwan inabi!”
7 Da ya ɓamɓare hatimi na huɗu, na ji muryar rayayyiyar halittan nan ta huɗu ta ce, “Zo.”
8 Da na duba, ga doki kili, sunan mahayinsa kuwa Mutuwa, Hades kuma tana biye da shi. Sai aka ba su iko a kan rubu'in duniya, su yi kisa da takobi, da yunwa, da annoba, da kuma namomin jeji na duniya.