1 Mala'ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga wani tauraron da ya faɗa a kan duniya daga sama, aka ba shi mabuɗin ramin mahallaka.
2 Ya kuwa buɗe ramin mahallakar, sai wani hayaƙi kamar na babbar matoya ya taso, har hayaƙin ramin nan ya duhunta rana da sararin sama.
3 Fāri suka fito zuwa cikin duniya daga cikin hayaƙin nan, aka ba su ikon harbi, irin na kunamin duniya.
4 Aka kuwa hana su cutar ciyayin duniya, ko tsiro, ko kowane itace, sai dai mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu.
5 Aka kuwa yardar musu su yi musu azaba har wata biyar, amma kada su kashe su, azabarsu kuwa, kamar ta kunama take, in ta harbi mutum.
6 A waɗannan kwanaki kuwa mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba, za su ƙagauta su mutu, mutuwa kuwa sai ta guje musu.