32 Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga zatinsa, nan da nan kuwa zai ɗaukaka shi.
33 Ya ku 'ya'yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu.
34 Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna.
35 Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”
36 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.”
37 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.”
38 Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.”