22 Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa'an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku.
23 A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana.
24 Har yanzu dai ba ku roƙi kome da sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”
25 “Duk wannan na faɗa muku da misalai ne. Lokaci yana zuwa da ba zan ƙara faɗa muku kome da misalai ba, sai dai in ba ku labarin Uba a sarari.
26 A ran nan za ku yi roƙo da sunana. Ban kuwa ce muku zan roƙar muku Uba ba,
27 domin shi Uban kansa na ƙaunarku, domin kun ƙaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito.
28 Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”