7 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Shari'a, bisa ga Sharian nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.”
8 Da Bilatus ya ji maganan nan sai ya ƙara tsorata.
9 Ya sāke shiga fāda, ya ce wa Yesu, “Daga ina kake?” Amma Yesu bai amsa masa ba.
10 Saboda haka Bilatus ya ce masa, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka sani ba ni ne da ikon sakinka, ko gicciye ka?”
11 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina in ba an ba ka daga Sama ba, saboda haka wanda ya bāshe ni gare ka ya fi ka zunubi.”
12 A kan wannan Bilatus ya nemi ya sake shi, sai dai Yahudawa suka ɗau kururuwa suna cewa, “In dai ka saki wannan, kai ba masoyin Kaisar ba ne. Ai, kowa ya mai da kansa sarki, ya tayar wa Kaisar ke nan.”
13 Da Bilatus ya ji wannan magana, sai ya fito da Yesu, ya zauna a kan gadon shari'a, wurin da ake kira Daɓe, da Yahudanci kuwa, Gabbata.