40 Ga shi yanzu, kuna neman kashe ni, ni mutumin da na gaya muku gaskiyar da na ji wurin Allah. Ba haka Ibrahim ya yi ba.
41 Ku kuna aikin da ubanku yake yi ne.” Suka ce masa, “Ba a haife mu daga fasikanci ba, ubanmu ɗaya ne, wato Allah.”
42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, domin daga wurin Allah na fito, ga ni nan kuwa. Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni.
43 Don me ba kwa gane maganata? Don ba kwa iya jimirin jin maganata ne.
44 Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.
45 Amma domin ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni.
46 A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya nake faɗa, to, don me ba kwa gaskata ni?