9 Wata rana a Shilo bayan da sun gama cin abinci, sai Hannatu ta tashi. Eli, firist, kuwa yana zaune a kujera a bakin ƙofar masujadar Ubangiji.
10 Hannatu tana fama da baƙin ciki ƙwarai, sai ta yi addu'a, tana kuka da ƙarfi ga Ubangiji.
11 Ta yi wa'adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.”
12 Eli kuwa ya lura da bakin Hannatu sa'ad da take yin addu'a.
13 Gama ta yi addu'ar a zuci, ba a jin muryarta, sai dai leɓun motsi. Don haka Eli ya zaci tana maye ne,
14 ya kuwa ce mata, “Sai yaushe za ki daina maye? Ki daina shan ruwan inabi.”
15 Hannatu kuwa ta amsa ta ce, “Ba haka ba, ya shugabana, ni mace ce da take baƙin ciki ƙwarai. Ni ban sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa maye ba, amma ina faɗa wa Ubangiji dukan abin da yake a zuciyata.