12 Jama'ar Isra'ila kuwa suka ce wa Sama'ila, “Su wa suka ce Saul ba zai sarauce mu ba? Ka kawo su, mu kashe su.”
13 Amma Saul ya ce, “Ba wanda za a kashe a yau, gama Ubangiji ya yi wa Isra'ila ceto a yau.”
14 Sai Sama'ila ya ce wa jama'a, “Ku zo, mu tafi Gilgal a yi wankan sarautar a can.”
15 Jama'a duka kuwa suka nufi Gilgal, suka yi wa Saul wankan sarauta a gaban Ubangiji. Suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama. A can kuwa Saul tare da dukan mutanen Isra'ila suka yi murna ƙwarai.