20 Saboda haka kowane Ba'isra'ile yakan gangara zuwa Filistiyawa domin ya koɗa bakin garmarsa, da fartanyasa, da gatarinsa, da laujensa,
21 duk lokacin da za su koɗar bakin garma da fartanya sai su biya sulusin shekel ne, ladan koɗar gatari da shirya abin korar shanun noma sulusin shekel ne.
22 A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko mashi ba a cikin mutanen da suke tare da Saul da Jonatan. Amma Saul da ɗansa, Jonatan, suna da su.
23 Sai ƙungiyar sojojin Filistiyawa ta fita zuwa mashigin Mikmash.