13 Sa'an nan Jonatan ya hau dutsen da rarrafe, mai ɗaukar makamansa kuwa yana biye da shi. Jonatan ya fāɗa wa Filistiyawa, ya yi ta kā da su, mai ɗaukar makamansa kuma ya bi bayansa yana ta karkashe su.
14 A wannan karo na farko Jonatan da mai ɗaukar makamansa suka kashe mutum wajen ashirin a wani fili mai fāɗi kamar rabin kadada.
15 Dukan Filistiyawan da suke a filin suka ji tsoro, da mahara da sauran sojoji suka yi rawar jiki, ƙasa ta girgiza, aka yi babbar gigicewa.
16 Da matsara na Saul a Gibeya ta Biliyaminu suka duba, sai ga taron Filistiyawa ya watse, kowa ya nufi wajensa, suna tafiya barkatai.
17 Saul ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ƙidaya mutane yanzu don ku ga wanda ya fita daga cikinmu.” Da aka ƙirga mutanen sai aka tarar Jonatan da mai ɗaukar makamansa ba su nan.
18 Sai Saul ya ce wa Ahaija, “Kawo akwatin alkawarin Allah a nan.” Gama a wannan lokaci akwatin Allah yana hannun Isra'ilawa.
19 Sa'ad da Saul yake magana da firist ɗin, sai hargowa a sansanin Filistiyawa ta yi ta ƙaruwa, Saul kuwa ya ce wa firist, “Janye hannunka.”