48 Ya yi aikin jaruntaka, ya bugi Amalekawa, ya ceci Isra'ilawa daga hannun dukan waɗanda suka taso musu.
49 'Ya'yan Saul, maza ke nan, Jonatan, da Yishwi, da Malkishuwa. Yana kuma da 'ya'ya mata biyu, Merab, 'yar fari, da Mikal.
50 Sunan matarsa kuwa Ahinowam 'yar Ahimawaz. Sunan shugaban rundunansa kuwa Abner ne, ɗan Ner, kawunsa.
51 Kish mahaifin Saul, da Ner mahaifin Abner, 'ya'yan Abiyel ne.
52 Saul ya yi ta yaƙi mai zafi da Filistiyawa dukan zamanin da yake sarauta. Idan Saul ya ga ƙaƙƙarfan mutum, ko jarumi, sai ya sa shi cikin sojansa.