5 Ɗaya dutsen yana wajen arewa a gaban Mikmash, ɗayan kuma yana daga kudu a gaban Geba.
6 Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.”
7 Sai mai ɗaukar masa makamai ya ce, “Ka yi abin da yake a zuciyarka, ga shi, ina tare da kai, gama ina goyon bayanka, kamar yadda zuciyarka take haka kuma tawa.”
8 Sa'an nan Jonatan ya ce, “Za mu haye zuwa wurin mutanen, mu nuna kanmu gare su.
9 Idan sun ce mana, ‘Ku dakata har mu zo wurinku,’ to, sai mu tsaya cik, ba za mu tafi wurinsu ba.
10 Amma idan sun ce, ‘Ku haura zuwa wurinmu,’ to, sai mu haura, gama wannan alama ce, wato Ubangiji ya bashe su a hannunmu.”
11 Sai su biyu suka tafi suka nuna kansu ga sansanin Filistiyawa. Da Filistiyawa suka gan su, sai suka ce, “Ku duba, Ibraniyawa suna fitowa daga cikin ramummuka inda suka ɓuya.”