10 Saul kuwa ya yi shiri ya nashi Dawuda, ya kafe shi ga bango. Da ya nashe shi, sai ya goce, mashin ya sami bangon. Dawuda kuwa ya gudu, ya tsere.
11 A daren nan Saul ya aiki manzanni su je gidan Dawuda don su yi fakonsa, su kashe shi da safe. Amma Mikal, matar Dawuda, ta faɗa masa cewa, “Idan ba ka gudu da daren nan ba, gobe za a kashe ka.”
12 Sai ta zurarar da Dawuda ta taga, ya gudu, ya tsere.
13 Mikal kuwa ta ɗauki kan gida ta kwantar da shi a gado, ta kuma sa masa matashin kai na gashin awaki, sa'an nan ta lulluɓe shi da mayafi.
14 Sa'ad da manzannin Saul suka zo don su kama Dawuda, sai ta ce musu, “Ba shi da lafiya.”
15 Saul kuma ya sāke aiken manzannin su tafi su ga Dawuda, ya ce musu, “Ku kawo shi nan wurina a kan gadonsa don in kashe shi.”
16 Da manzannin suka tafi, sai suka tarar da kan gida a gadon, da matashin kai na gashin awaki wajen kansa.