2 “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji,Babu wani mai kama da shi,Ba mai kiyaye mu kamar Allahnmu.
3 Kada ku ƙara yin magana ta girmankai,Ku daina maganganunku na fariya,Gama Ubangiji Allah shi ne masani,Yana kuma auna dukkan aikin da mutum ya yi.
4 An kakkarya bakunan ƙarfafan sojoji,Amma rarrauna ya zama mai ƙarfi.
5 Ƙosassun mutane suna ƙodago saboda abinci,Masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa.Bakarariya ta haifi 'ya'ya bakwai,Wadda ta haifi 'ya'ya da yawa kuwata rasa su duka.
6 Ubangiji ne yake kashewa, ya kuma rayar,Yana kai mutane kabari,Ya kuma tā da su.
7 Yakan sa waɗansu mutane su zamamatalauta,Waɗansu kuwa attajirai.Yakan ƙasƙantar da waɗansu,Ya kuma ɗaukaka waɗansu.
8 Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura,Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki.Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki,Ya ɗora su a wurare masu maƙami.Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne,A kansu ya kafa duniya.