28 Na zaɓi iyalinsa daga dukan kabilan Isra'ila domin su zama firistocina, su riƙa aiki a bagade, suna ƙona turare, su riƙa ɗaukar keɓaɓɓen akwatina cikin yi mini aiki. Na kuma yardar musu su sami rabonsu daga hadayun da aka ƙona a kan bagade.
29 Me ya sa kuke haɗama a kan hadayuna da sadakokin da na umarta? Eli, don me kake girmama 'ya'yanka fiye da ni, ka bar su suna ta cinye rabo mafi kyau na hadayun jama'ata Isra'ila?
30 Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.
31 Ga shi, lokaci yana zuwa da zan karkashe samari cikin iyalinka da danginka, har da ba za a sami wanda zai rayu har ya tsufa a gidanka ba.
32 Za ka kasance da damuwa da jin kishi, za ka duba dukan albarkun da zan sa wa Isra'ila, amma a gidanka ba za a taɓa samun wanda zai rayu har ya tsufa ba.
33 Zan dai bar ɗaya daga zuriyarka da rai, zai yi mini aikin firist, amma zai makance ya fid da zuciya ga kome. Dukan sauran zuriyarka kuwa za su yi mutuwa ƙarfi da yaji.
34 Lokacin da 'ya'yanka biyu, Hofni da Finehas, za su mutu rana ɗaya wannan zai nuna maka abin da na faɗa sai ya cika.