6 Ubangiji ne yake kashewa, ya kuma rayar,Yana kai mutane kabari,Ya kuma tā da su.
7 Yakan sa waɗansu mutane su zamamatalauta,Waɗansu kuwa attajirai.Yakan ƙasƙantar da waɗansu,Ya kuma ɗaukaka waɗansu.
8 Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura,Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki.Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki,Ya ɗora su a wurare masu maƙami.Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne,A kansu ya kafa duniya.
9 “Zai kiyaye rayukan amintattunmutanensa,Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu,Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.
10 Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji,Zai yi musu tsawa daga Sama.Ubangiji zai hukunta dukan duniya,Zai ba sarkinsa iko,Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zamamai nasara.”
11 Sa'an nan Elkana ya koma gidansa a Rama, amma yaron ya zauna a Shilo, yana aikin Ubangiji a hannun Eli, firist.
12 'Ya'yan Eli, maza kuwa, ba su da kirki, ba su kula da Ubangiji ba,