10 Sa'an nan Dawuda ya ce wa Jonatan, “Wane ne zai faɗa mini idan mahaifinka ya amsa maka da fushi?”
11 Jonatan kuwa ya ce masa, “Zo mu tafi saura.” Sai su biyu suka tafi saura.
12 Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Ubangiji Allah na Isra'ila zai zama shaida. Gobe war haka, ko jibi zan tattauna maganar da mahaifina, idan da nufin alheri zuwa gare ka, zan aika, in faɗa maka.
13 Amma idan har mahaifina yana da niyyar yi maka mugunta, amma ban sanar da kai ba, to, bari Ubangiji ya hukunta ni. Ubangiji ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina.
14 Ba lokacin da nake da rai ne kaɗai za ka nuna mini alherin Ubangiji domin kada in mutu ba.
15 Ko bayan raina kada ka daina nuna wa gidana alheri har abada, lokacin da Ubangiji ya datse maƙiyanka daga fuskar duniya.”
16 Jonatan ya yi alkawari da gidan Dawuda. Ubangiji kuwa zai ɗauki fansa a kan maƙiyan Dawuda.