31 Muddin ɗan Yesse na da rai a duniya, ba za ka kahu ba. Sarautarka kuma ba za ta kahu ba. Yanzu sai ka je ka taho mini da shi. Dole kashe shi za a yi.”
32 Jonatan ya ce wa mahaifinsa, “Me ya sa za a kashe shi? Me ya yi?”
33 Sai Saul ya jefe shi da mashi don ya kashe shi. Sai Jonatan ya gane lalle mahaifinsa ya yi niyya ya kashe Dawuda.
34 Sai Jonatan ya tashi da fushi daga wurin cin abinci, bai ci abinci a rana ta biyu ga watan ba, saboda baƙin ciki a kan Dawuda, domin kuma mahaifinsa ya kunyata shi.
35 Da safe Jonatan ya tafi saura tare da wani yaro daidai lokacin da ya shirya da Dawuda.
36 Sai ya ce wa yaron, “Yi gudu, ka nemo kiban da zan harba.” Sa'ad da yaron ya ruga, sai ya harba kibiya gaba da shi.
37 Da yaron ya kai inda Jonatan ya harba kibiyar, sai ya ce masa, “Ba kibiyar tana a gaban ka ba?”