1 Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da 'yan'uwansa da mutanen gidan ubansa, suka ji labari, suka tafi can wurinsa.
2 Kowane mutum kuma da yake matse, da wanda ake bi bashi, da wanda ransa ba ya kwance, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Sun kai wajen mutum ɗari huɗu.
3 Daga can Dawuda ya wuce zuwa Mizfa ta Mowab. Ya ce wa Sarkin Mowab, “Ina roƙonka, ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Ubangiji zai yi da ni.”
4 Sai ya bar iyayensa a wurin Sarkin Mowab, suka zauna a wurinsa duk lokacin da Dawuda yake ta ɓuya a kogwannin duwatsu.
5 Sa'an nan Gad, annabi, ya ce wa Dawuda, “Kada ka zauna a nan, maza ka tafi ƙasar Yahuza.” Sai ya tashi, ya tafi kurmin Haret.
6 Sai Saul ya ji labari an gane inda Dawuda da mutanensa suke. Saul kuwa yana zaune a Gibeya a gindin itacen tsamiya a kan tudu, yana riƙe da mashinsa. Dukan fādawansa suna tsaye kewaye da shi.