18 Su biyu fa suka yi wa juna alkawari a gaban Ubangiji. Dawuda ya zauna a Horesh, Jonatan kuwa ya koma gida.
19 Sai Zifawa suka haura zuwa wurin Saul a Gibeya, suka ce masa, “Dawuda ya ɓuya a ƙasarmu cikin Horesh a kan tudun Hakila da yake kudu da jejin Yahuza.
20 Sai ka gangara, ka zo, ya sarki, ta yadda kake so. Mu za mu bashe shi a hannun sarki.”
21 Saul ya ce, “Ubangiji ya sa muku albarka, gama kuna jin juyayina.
22 Ku tafi, ku ƙara tabbatar da inda ya ɓuya, da wanda ya gan shi a wurin, gama an faɗa mini, cewa shi mai wayo ne.
23 Ku lura sosai da dukan wuraren da yake ɓuya, sa'an nan ku komo mini da tabbataccen labari. Sa'an nan zan tafi tare da ku. Idan yana ƙasar, zan neme shi ko'ina a ƙasar Yahuza.”
24 Sai suka yi gaba, suka tafi Zif. Dawuda da mutanensa kuwa suna jejin Mawon, cikin Araba, kudu da Yeshimon.