8 Saul ya kirawo dukan mutanensa, su fita yaƙi, su tafi Kaila don su kewaye Dawuda tare da mutanensa.
9 Dawuda kuwa ya sani Saul yana shirya hanyar kashe shi, sai ya ce wa Abiyata, firist, “Kawo falmaran a nan.”
10 Sa'an nan ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, hakika bawanka ya ji Saul yana niyyar zuwa Kaila don ya hallakar da garin saboda ni.
11 Ko mutanen Kaila za su bashe ni a hannunsa? Ko Saul zai zo kamar yadda na ji? Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ina roƙonka ka faɗa wa bawanka.”Ubangiji kuwa ya ce, “Saul zai zo.”
12 Dawuda kuma ya ce, “Mutanen Kaila za su bashe ni da mutanena a hannun Saul?”Ubangiji ya ce masa, “Za su bashe ku.”
13 Sa'an nan Dawuda da mutanen da suke tare da shi, mutum wajen ɗari shida, suka tashi daga Kaila, suka tafi inda hali ya kai su. Da Saul ya ji Dawuda ya tsere daga Kaila, sai ya fasa tafiya can.
14 Dawuda ya zauna a ɓoye cikin jeji a ƙasar tudu ta jejin Zif. Saul kuwa ya yi ta nemansa kowace rana, amma Ubangiji bai ba da Dawuda a hannunsa ba.