3 Sunan mutumin kuwa Nabal, sunan matarsa kuma Abigail, ita haziƙa ce, kyakkyawa, amma mijinta miskili ne, marar mutunci. Shi daga zuriyar Kalibu ne.
4 Daga cikin jeji, Dawuda ya ji, wai Nabal yana yi wa tumakinsa sausaya,
5 sai ya aiki samari goma, ya ce musu, “Ku tafi Karmel wurin Nabal, ku ce ina gaishe shi.
6 Gaisuwar da za ku yi masa ke nan, ku ce, ‘Salama gare ka, salama ga gidanka, salama kuma ga dukan abin da kake da shi.
7 Na ji kana da masu sausaya. Lokacin da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, ba abin da ya ɓace musu dukan lokacin da suke a Karmel.
8 Tambayi samarinka, za su faɗa maka. Saboda haka ka yarda samarina su sami tagomashi a wurinka, gama yau ranar biki ce. Muna roƙonka ka ba barorinka, da ɗanka, Dawuda abin da za ka iya ba mu.’ ”
9 Sa'ad da samarin Dawuda suka zo, suka faɗa wa Nabal dukan abin da Dawuda ya ce musu, sai suka dakata.