11 Sai matar ta ce, “Wa kake so in hawar maka?”Ya ce, “Ki hawar mini da Sama'ila.”
12 Da matar ta ga Sama'ila, sai ta fasa ƙara, ta ce wa Saul, “Don me ka ruɗe ni, ashe, kai ne sarki Saul?”
13 Sarki kuwa ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, me kike gani?”Ta ce masa, “Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa.”
14 Ya ce mata, “Yaya kamanninsa yake?”Ta ce, “Wani tsoho ne yake hawowa, yana naɗe da alkyabba.”Saul ya gane Sama'ila ne, sai ya sunkuyar da kai, ya durƙusa har ƙasa da bangirma.
15 Sai Sama'ila ya ce wa Saul, “Don me ka dame ni, ka hawar da ni?”Saul ya ce, “Ina cikin babbar wahala, gama Filistiyawa suna yaƙi da ni, Allah kuma ya rabu da ni, ya ƙi amsa mini ko ta wurin annabawa ko ta mafarkai, saboda haka na kira ka, ka faɗa mini abin da zan yi.”
16 Sai Sama'ila ya ce masa, “Don me za ka tambaye ni, tun da yake Ubangiji ya rabu da kai, ya zama magabcinka?
17 Ai, abin da Ubangiji ya faɗa mini a kanka, shi ne ya cika, gama Ubangiji ya fizge mulki daga hannunka, ya ba maƙwabcinka Dawuda.