20 Da jin maganar Sama'ila sai Saul ya faɗi ƙasa warwar. Tsoro ya kama shi ƙwarai. Ba shi kuma da ƙarfi domin bai ci kome dukan yini da dukan dare ba.
21 Sai matar ta zo wurin Saul, da ta ga ya tsorata, sai ta ce masa, “Baiwarka ta yi kasai da ranta, ta kuwa kasa kunne gare ka.
22 To, kai ma ka kasa kunne ga baiwarka. Bari in ba ka abinci, ka ci don ka sami ƙarfin tafiya.”
23 Sai ya ƙi, ya ce, “Ba zan ci abinci ba.” Sai da barorinsa da matar suka roƙe shi, sa'an nan ya ji maganarsu, ya tashi daga ƙasa, ya zauna a bakin gado.
24 Matar kuwa ta yi hanzari ta yanka turkakken maraƙinta, ta ɗauki gari ta kwaɓa, ta toya abinci marar yisti da shi.
25 Sa'an nan ta kawo wa Saul da barorinsa, suka ci, sa'an nan suka tashi suka tafi da daren nan.