6 Akish kuwa ya kira Dawuda, ya ce masa, “Kai amintacce ne a ganina, daidai ne kuma ka tafi yaƙi tare da ni, gama ban same ka da wani laifi ba tun daga ranar zuwanka wurina har yau, duk da haka sarakunan ba su amince da kai ba.
7 To, sai ka koma ka isa lafiya, don kada ka tā da hankalin sarakunan Filistiyawa.”
8 Dawuda ya ce wa Akish, “Me na yi? Wane laifi ka samu a wurin baranka tun daga ranar da na shiga hidimarka har zuwa yau, da ba zan tafi in yi yaƙi da abokan gāban ubangijina sarki ba?”
9 Akish ya amsa wa Dawuda, ya ce, “A ganina kai marar laifi ne kamar mala'ikan Allah, duk da haka shugabannin sojojin Filistiyawa sun ce, ‘Ba zai tafi yaƙi tare da mu ba.’
10 Ka tashi da sassafe kai da barorin ubangijinka da suka zo tare da kai. Da gari ya waye sai ku kama hanya.”
11 Dawuda kuwa ya tashi da sassafe ya kama hanya tare da mutanensa zuwa ƙasar Filistiyawa, amma Filistiyawa suka haura zuwa Yezreyel.