18 Dawuda ya ƙwato dukan abin da Amalekawa suka kwashe, har da matansa biyu.
19 Ba abin da ya ɓace, ƙanƙane ko babba, ko cikin 'ya'ya mata da maza, ko kuwa wani abu daga cikin ganimar, duk Dawuda ya komar da su.
20 Ya kuma ƙwato garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu. Mutanensa suka koro shanun, suka yi gaba, suka ce, “Wannan shi ne ganimar Dawuda.”
21 Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bar su a rafin Besor, sai suka tafi su taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa'ad da Dawuda ya zo kusa da su ya gaishe su.
22 Sai dukan mugaye da marasa kirki daga cikin mutanen da suka tafi tare da Dawuda suka ce, “Tun da yake ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su kome daga cikin ganimar da muka ƙwato ba, sai dai kowane mutum ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa ya tafi.”
23 Amma Dawuda ya ce, “'Yan'uwana, ba za ku yi haka da abin da Ubangiji ya ba mu ba. Ubangiji ya kiyaye mu, ya kuma ba da maharan da suka washe mu a hannunmu.
24 Wa zai goyi bayanku a kan wannan al'amari? Wanda ya tafi wurin yaƙi da wanda ya zauna wurin kaya rabonsu zai zama daidai da juna.”