4 Sai suka aika zuwa Shilo aka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Mai Runduna, wanda yake zaune a tsakanin kerubobi. 'Ya'yan nan na Eli, maza guda biyu, wato Hofni da Finehas, suna tare da akwatin alkawarin.
5 Da akwatin alkawarin Ubangiji ya iso sansanin, sai dukan mutanen Isra'ila suka yi sowa da ƙarfi, har ƙasa ta amsa.
6 Da Filistiyawa suka ji amon sowar suka ce, “Ina ma'anar irin wannan babbar sowa a sansanin Ibraniyawa?” Da suka gane akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga sansanin,
7 sai Filistiyawa suka tsorata, suka ce, “Allah ya shiga sansanin, kaitonmu, gama ba a taɓa yin irin wannan abu ba.
8 Mun shiga uku, wa zai cece mu daga hannun allolin nan masu iko? Waɗannan suka karkashe Masarawa a hamada!
9 Ya ku Filistiyawa, ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka don kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suka zama bayinku, ku yi jaruntaka ku yi yaƙi.”
10 Filistiyawa kuwa suka yi yaƙi gadan-gadan, suka ci mutanen Isra'ila. Mutanen Isra'ila suka gudu, kowa ya nufi gidansa. Aka kashe Isra'ilawa da yawa, wato mutum dubu talatin (30,000).