1 Sa'ad da Filistiyawa suka ƙwace akwatin alkawarin Allah a Ebenezer, suka kai shi Ashdod.
2 Suka shigar da shi cikin haikalin gunkinsu, Dagon, suka ajiye shi kusa da gunkin.
3 Kashegari da safe sa'ad da mutanen Ashdod suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Suka ta da shi, suka ajiye a wurinsa.
4 Kashegari da safe kuma da suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Kan Dagon da hannuwansa a gutsure, suna nan a dokin ƙofa. Gangar jikin ce ta ragu.
5 (Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba su taka dokin ƙafar Dagon a Ashdod ba har wa yau.)
6 Ubangiji kuwa ya hukunta mutanen Ashdod ƙwarai da gaske, ya kuma razanar da su, ya azabtar da su da marurai, su da na kewaye da su.
7 Da mutanen Ashdod suka ga yadda abin yake, sai suka ce, “Kada a bar akwatin alkawarin Allah na Isra'ila tare da mu, gama ya tsananta mana, mu da Dagon, allahnmu.”