17 Zai kuma karɓi ushirin dabbobinku. Za ku zama barorinsa.
18 A lokacin za ku yi kuka saboda sarkin da kuka zaɓar wa kanku, amma Ubangiji ba zai kasa kunne ga kukanku ba.”
19 Amma mutane suka ƙi jin abin da Sama'ila ya faɗa musu, sai suka ce, “Duk da haka dai, muna so sarki ya sarauce mu,
20 don mu ma mu zama kamar sauran ƙasashe, mu sami sarki wanda zai sarauce mu, ya shugabance mu zuwa yaƙe-yaƙe.”
21 Sa'ad da Sama'ila ya ji dukan abin da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.
22 Ubangiji kuwa ya ce wa Sama'ila, “Ka yarda da abin da suka ce, ka naɗa musu sarki.”Sai Sama'ila ya ce wa mutanen Isra'ila, “Kowa ya koma gida.”