26 Sulemanu kuwa ya tattara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), waɗanda ya zaunar da su a biranen karusai da kuma waɗansu tare da shi a Urushalima.
27 Sarki ya sa azurfa ta gama gari, kamar dai duwatsu a Urushalima, itacen al'ul kuma ya zama kamar jumaiza na Shefela.
28 Sulemanu kuwa ya sayo dawakai daga Masar da Kuye. 'Yan kasuwar sarki sukan sayo dawakai daga Kuye a kan tamaninsu.
29 Akan sayo karusa a Masar a bakin azurfa ɗari shida, doki kuwa a bakin ɗari da hamsin, 'yan kasuwar sarki sukan sayar da su ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa.