22 Amma Fir'auna ya ce masa, “Me ka rasa a nan har da kake so ka koma ƙasarka?”Hadad ya ce masa, “Ka dai yardar mini kawai in tafi.” Ya kuwa koma ƙasarsa.
23 Allah kuma ya sa Rezon ɗan Eliyada, ya tayar wa Sulemanu, shi Rezon ya gudu daga wurin maigidansa, Hadadezer Sarkin Zoba.
24 Ya tattara wa kansa mutane ya zama shugaban 'yan hari bayan kashe-kashen da Dawuda ya yi. Sai suka tafi Dimashƙu, suka zauna a can, suka naɗa shi Sarkin Dimashƙu.
25 Ya zama abokin gāban Isra'ila a dukan zamanin Sulemanu. Ya yi ta ɓarna kamar yadda Hadad ya yi. Ya ƙi jinin mutane Isra'ila. Ya yi mulkin suriya.
26 Sai Yerobowam ɗan Nebat, Ba'ifraime na Zaretan, baran Sulemanu, wanda sunan mahaifiyarsa Zeruya, wadda mijinta ya rasu, shi ma ya tayar wa sarki.
27 Ga dalilin da ya sa ya tayar wa sarki.Sulemanu ya gina Millo ya kuma faɗaɗa garun birnin Dawuda tsohonsa.
28 Yerobowam mutum ne mai fasaha. Da Sulemanu ya ga shi saurayi ne mai himma, sai ya shugabantar da shi kan aikin tilas na gidan Yusufu.