26 Sai Yerobowam ɗan Nebat, Ba'ifraime na Zaretan, baran Sulemanu, wanda sunan mahaifiyarsa Zeruya, wadda mijinta ya rasu, shi ma ya tayar wa sarki.
27 Ga dalilin da ya sa ya tayar wa sarki.Sulemanu ya gina Millo ya kuma faɗaɗa garun birnin Dawuda tsohonsa.
28 Yerobowam mutum ne mai fasaha. Da Sulemanu ya ga shi saurayi ne mai himma, sai ya shugabantar da shi kan aikin tilas na gidan Yusufu.
29 A sa'ad da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahija mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahija yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai,
30 sai Ahija ya kama sabuwar rigar da ya sa, ya kyakketa ta ƙyalle goma sha biyu,
31 ya ce wa Yerobowam, “Kwashi ƙyalle goma, gama haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, ina gab da in kece sarauta daga hannun Sulemanu, zan ba ka kabila goma.
32 Amma Sulemanu, zai sami kabila ɗaya saboda bawana Dawuda, da kuma ɗaya saboda Urushalima, wato birnin da na zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka.