5 Gama Sulemanu ya bi Ashtoret ta Sidoniyawa, da Milkom, wato gunkin Ammonawa.
6 Ya yi wa Ubangiji zunubi. Bai bi Ubangiji da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.
7 Sulemanu ya gina wa Kemosh, wato gunkin Mowab, da Molek, gunkin Ammonawa, masujadai a kan dutsen da yake gabas da Urushalima.
8 Ya kuma gina masujadai inda dukan matansa baƙi za su riƙa miƙa turare da hadayu ga gumakansu.
9 Ubangiji kuwa ya yi fushi da Sulemanu, domin zuciyar Sulemanu ta rabu da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya bayyana a gare shi sau biyu,
10 ya kuma umarce shi kada ya bi gumaka. Amma bai kiyaye umarnin da Ubangiji ya yi masa ba.
11 Saboda haka Ubangiji ya ce wa Sulemanu, “Tun da yake ka yi haka, ba ka kuwa kiyaye umarnina da dokokina waɗanda na umarce ka da su ba, to, hakika zan ƙwace mulki daga gare ka, in ba baranka.