25 Mutane suka wuce, suka ga gawar a kan hanya, da zaki a tsaye kusa da gawar. Suka tafi suka faɗa a birni, inda tsohon annabin nan yake.
26 Sa'ad da tsohon annabin nan ya ji, sai ya ce, “Wannan annabin Allah ne, wanda bai yi biyayya da maganar Ubangiji ba, saboda haka Ubangiji ya bashe shi ga zaki ya yayyage shi, ya kashe shi, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.”
27 Sa'an nan ya ce wa 'ya'yansa maza, “Ku ɗaura mini shimfiɗa.” Su kuwa suka ɗaura,
28 ya hau ya tafi, ya iske gawar a hanya. Jakin da zakin suna tsaye kusa da gawar. Zakin bai ci gawar ba, bai kuma fāɗa wa jakin ba.
29 Tsohon annabin kuwa ya ɗauki gawar ya ɗora bisa jakin, ya kawo ta cikin birni, wato Betel, don yin makoki da binnewa.
30 Ya binne gawar a kabarinsa, sa'an nan suka yi makoki suna cewa, “Kaito, dan'uwana!”
31 Bayan da ya binne shi, sai ya ce wa 'ya'yansa, “Sa'ad da na rasu, sai ku binne ni a kabarin da aka binne annabin nan. Ku ajiye gawata kusa da tasa.