27 A maimakonsu kuwa sarki Rehobowam ya yi garkuwoyin tagulla, ya sa a hannun shugabannin masu tsaro waɗanda suke tsaron ƙofar gidan sarki.
28 Duk lokacin da sarki ya shiga Haikalin Ubangiji, sai matsara su ɗauki garkuwoyin, su kuma mayar da su a ɗakin tsaro.
29 Sauran ayyukan Rehobowam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
30 Kullum akan yi ta yin yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam,
31 Rehobowam kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce. Ɗansa, Abaija ya gāji sarautar.