6 Da Ahija ya ji motsin takawarta a bakin ƙofa, sai ya ce mata, “Ki shigo, matar Yerobowam, me ya sa kike yi kamar ke wata ce dabam? Gama an umarce ni in faɗa miki labari marar daɗi.
7 Ki koma, ki faɗa wa Yerobowam, Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Na ɗaukaka ka daga cikin mutane, na sa ka zama shugaban mutanena, Isra'ilawa.
8 Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba ka, duk da haka ba ka zama kamar bawana Dawuda ba, wanda ya kiyaye umarnaina, ya bi ni da zuciya ɗaya, yana yin abin da yake daidai a gare ni.
9 Amma ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka riga ka, ka yi wa kanka gumaka, da siffofi na zubi, ka tsokane ni in yi fushi, ka yi watsi da ni.
10 Saboda haka zan kawo masifa a gidanka. Zan datse maka kowane ɗa namiji, ko bawa, ko 'yantacce, daga cikin Isra'ila. Zan ƙone gidanka kamar yadda akan ƙone juji ƙurmus.
11 Duk wanda yake naka wanda zai mutu a birni, karnuka za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura tsuntsaye za su cinye shi, ni Ubangiji, ni ne na faɗa.’
12 “Ki tashi, ki koma gida. Da shigarki birni, yaron zai mutu.