12 Ya kori mata da maza da suke karuwanci a wuraren tsafi na arna a ƙasar, ya kuma kawar da gumakan da kakanninsa suka yi.
13 Ya kuma fitar da tsohuwarsa Ma'aka daga zaman sarauniya, domin ta yi ƙazantacciyar siffa ta gunkiyar Ashtoret. Asa ya sassare siffar, ya ƙone ta a rafin Kidron.
14 Amma ba a kawar da wuraren tsafi na tuddai ba, duk da haka Asa ya yi aminci sosai ga Ubangiji dukan kwanakinsa.
15 Ya kawo dukan tsarkakakkun abubuwan da tsohonsa ya keɓe, da kuma azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda shi kansa ya yi, a cikin Haikalin Ubangiji.
16 Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa da Ba'asha, Sarkin Isra'ila a dukan kwanakin mulkinsu.
17 Ba'asha, Sarkin Isra'ila, ya kai wa Yahuza yaƙi. Sai ya gina Rama don ya hana kowa ya fita ko kuma ya shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza.
18 Sa'an nan Asa ya kwashe dukan azurfa da zinariya da suka ragu a ɗakunan ajiya na Haikalin Ubangiji, da na gidan sarki, ya ba barorinsa su kai wa Ben-hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, ya ce,