1 Sar 20:31-37 HAU

31 Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra'ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa'an nan mu tafi wurin Sarkin Isra'ila, watakila zai bar ka da rai.”

32 Sai suka sa tufafin makoki, suka ɗaura igiyoyi a wuyansu, suka tafi wurin Sarkin Isra'ila, suka ce, “Baranka, Ben-hadad, yana roƙonka ka bar shi da rai.”Ahab kuwa ya amsa ya ce, “Har yanzu yana da rai? Ai, shi kamar ɗan'uwana ne.”

33 Da ma abin da fādawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan'uwanka, Ben-hadad.”Sarki Ahab ya ce musu, “Ku je ku kawo shi.” Ben-hadad kuwa ya zo wurinsa. Ahab ya sa ya shiga tare da shi cikin karusarsa.

34 Ben-hadad ya ce masa, “Biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, zan mayar maka. Kai kuma za ka yi karauku a Dimashƙu kamar yadda tsohonka ya yi a Samariya.”Sai Ahab ya ce, “Zan bar ka, ka tafi a kan wannan sharaɗi.” Ya kuwa yi alkawari da shi, sa'an nan ya bar shi, ya tafi.

35 Ubangiji ya umarci wani daga cikin annabawa ya ce wa abokinsa bisa ga umarnin Ubangiji, “Ina roƙonka ka buge ni.” Abokinsa kuwa ya ƙi ya buge shi.

36 Sai annabin ya ce wa wannan aboki, “Da yake ba ka yi biyayya da muryar Ubangiji ba, da tashinka daga wurina, zaki zai kashe ka.” Da ya tashi daga wurinsa, sai zaki ya gamu da shi, ya kashe shi.

37 Annabin kuma ya tarar da wani mutum, ya ce masa, “Ina roƙonka ka buge ni.” Mutumin kuwa ya buge shi da ƙarfi ya rotsa shi.