34 Ben-hadad ya ce masa, “Biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, zan mayar maka. Kai kuma za ka yi karauku a Dimashƙu kamar yadda tsohonka ya yi a Samariya.”Sai Ahab ya ce, “Zan bar ka, ka tafi a kan wannan sharaɗi.” Ya kuwa yi alkawari da shi, sa'an nan ya bar shi, ya tafi.
35 Ubangiji ya umarci wani daga cikin annabawa ya ce wa abokinsa bisa ga umarnin Ubangiji, “Ina roƙonka ka buge ni.” Abokinsa kuwa ya ƙi ya buge shi.
36 Sai annabin ya ce wa wannan aboki, “Da yake ba ka yi biyayya da muryar Ubangiji ba, da tashinka daga wurina, zaki zai kashe ka.” Da ya tashi daga wurinsa, sai zaki ya gamu da shi, ya kashe shi.
37 Annabin kuma ya tarar da wani mutum, ya ce masa, “Ina roƙonka ka buge ni.” Mutumin kuwa ya buge shi da ƙarfi ya rotsa shi.
38 Sai annabin ya ɓad da kama, ya ɗaure fuskarsa da ƙyalle, ya tafi, ya jira sarki a hanya.
39 Sa'ad da sarki yake wucewa, sai ya kira sarki, ya ce, “Ni baranka na tafi yaƙi, sai ga shi, soja ya kawo mini mutum, ya ce mini, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi ya kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’
40 Da na shiga fama da kai da kawowa sai mutumin ya tsere.”Sai Sarkin Isra'ila ya ce masa, “Haka shari'arka za ta zama, gama kai da kanka ka yanke shari'ar.”