39 Sa'ad da sarki yake wucewa, sai ya kira sarki, ya ce, “Ni baranka na tafi yaƙi, sai ga shi, soja ya kawo mini mutum, ya ce mini, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi ya kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’
40 Da na shiga fama da kai da kawowa sai mutumin ya tsere.”Sai Sarkin Isra'ila ya ce masa, “Haka shari'arka za ta zama, gama kai da kanka ka yanke shari'ar.”
41 Annabin ya yi saurim, ya kware ƙyallen a fuskarsa, sa'an nan sarki ya gane, ashe, ɗaya daga cikin annabawa ne.
42 Sa'an nan annabin ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ka bar mutumin da na ƙaddara ga mutuwa ya kuɓuta daga hannunka, haka ranka zai zama a maimakon nasa, mutanenka kuwa a maimakon mutanensa.’ ”
43 Sarkin Isra'ila kuwa ya tafi gidansa a Samariya da baƙin ciki.