5 Jakadun kuwa suka sāke komawa suka ce wa Ahab, “Ben-hadad ya ce, ‘Na aika maka ka ba ni azurfarka, da zinariyarka, da matanka, da 'ya'yanka.
6 Banda haka kuma zan aiko barorina wurinka gobe war haka su bincike gidanka da gidajen fādawanka, su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi da su.’ ”
7 Ahab Sarkin Isra'ila kuwa ya kirawo dukan dattawan ƙasar, ya ce, “Ku gani fa, ku duba yadda mutumin nan yake neman rikici, gama ya aiko don in ba shi matana, da 'ya'yana, da azurfata, da zinariyata, ni kuwa ban hana masa ba.”
8 Dukan dattawan da mutane, suka ce masa, “Kada ka kula, balle ka yarda.”
9 Sai ya ce wa jakadun Ben-hadad, “Ku ce wa maigirma, sarki, dukan abin da ya nema a wurina da farko, zan yi, amma wannan na ƙarshe, ban zan iya yi ba.”Jakadun kuwa suka koma da wannan labari.
10 Ben-hadad kuwa ya sāke aikawa wurinsa ya ce, “Bari alloli su kashe ni idan ban kai mutane da yawa da za su hallaka Samariya ba.”
11 Sarki Ahab ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, sojan ainihi, sai ya gama yaƙi sa'an nan ya yi fāriya, amma ba tun kafin a fara ba.”