26 Ya yi abar banƙyama ƙwarai, ya bi gumaka kamar yadda Amoriyawa suke yi, waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban Isra'ilawa.
27 Da Ahab ya ji wannan magana, sai ya yage tufafinsa, ya sa na makoki, ya yi azumi, ya kwanta a tsummokin makoki, ya tashi yana tafiya a hankali.
28 Ubangiji ya yi magana da Iliya Batishbe ya ce,
29 “Ka ga yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana? Da yake ya ƙasƙantar da kansa a gabana, ba zan kawo masifar a zamaninsa ba, sai a zamanin ɗansa ne, zan kawo masifar a kan gidansa.”