3 Amma Nabot ya ce wa Ahab, “Ubangiji ya sawwaƙa in ba ka gādon kakannina.”
4 Ahab ya koma gida da baƙin ciki da rai a ɓace saboda abin da Nabot Bayezreyele ya faɗa masa. Ahab ya kwanta a gadonsa, ya mai da fuskarsa bango ya ƙi cin abinci.
5 Yezebel, matarsa kuwa ta zo wurinsa, ta ce masa, “Me ya sa ka damu, ka ruɗe haka, har ka ƙi cin abinci?”
6 Ya ce mata, “Domin na yi magana da Nabot Bayezreyele, na ce ya sayar mini da gonar inabinsa, idan kuma yana so, sai in ba shi wata gonar inabi a maimakon tasa, amma ya ce ba zai ba ni gonar inabin ba.”
7 Yezebel, matarsa, ta ce masa, “Ba kai ne kake mulkin Isra'ila ba? Tashi, ka ci abinci, ka yi farin ciki, zan ba ka gonar inabin Nabot Bayezreyele.”
8 Sa'an nan ta rubuta wasiƙu da sunan Ahab, ta hatimce su da hatiminsa, sa'an nan ta aika da wasiƙun zuwa ga dattawa da fādawan da suke zaune a birnin tare da Nabot.
9 Ta rubuta a wasiƙun, “A yi shelar azumi, a sa Nabot a gaban jama'a.