1 Hiram, Sarkin Taya, ya aiki jakadunsa zuwa wurin Sulemanu, sa'ad da ya ji ya gāji tsohonsa, gama Hiram abokin Dawuda ne ƙwarai dukan kwanakinsa.
2 Sai Sulemanu ya aika wurin Hiram, ya ce,
3 “Ka sani tsohona, Dawuda, bai iya gina Haikalin yin sujada ga Ubangiji Allahnsa ba saboda fama da yaƙe-yaƙe da maƙiyan da suke kewaye da shi, kafin Ubangiji ya mallakar masa da su.
4 Amma yanzu Ubangiji Allahna ya hutasshe ni ta kowace fuska, ba fitina ko masifa.