7 Da Hiram ya ji maganar Sulemanu, sai ya yi murna ƙwarai, ya ce, “Yabo ga Ubangiji saboda wannan rana, gama ya ba Dawuda ɗa mai hikima da zai shugabanci wannan babbar jama'a.”
8 Sa'an nan Hiram ya aika wurin Sulemanu, ya ce, “Na ji saƙonka da ka aiko mini, a shirye nake in yi maka dukan abin da kake bukata a kan katakan itacen al'ul, da na fir.
9 Barorina za su kawo su daga Lebanon zuwa teku. Zan sa a yi gadon fito da su, su bi teku zuwa inda kake so, a can mutanena za su warware su, sa'an nan naka mutane su kwashe su. Kai kuma ka ba da abinci ga mutanena.”
10 Sai Hiram ya ba Sulemanu dukan katakan itacen al'ul da na fir da yake bukata,
11 Sulemanu kuwa yakan ba Hiram alkama mudu dubu ashirin (20,000), da tattaccen man zaitun ma'auni dubu ashirin (20,000) kowace shekara domin ya ciyar da mutanensa.
12 Ubangiji kuwa ya ba Sulemanu hikima kamar yadda ya yi masa alkawari. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Hiram da Sulemanu, suka kuma ƙulla yarjejeniya da juna.
13 Sarki Sulemanu kuwa ya sa a yi aikin tilas daga cikin Isra'ila duka. Waɗanda aka samu da za su yi aikin tilas ɗin mutum dubu talatin (30,000) ne.