13 Zan zauna tare da mutanena, wato Isra'ila, a wannan Haikali da kake ginawa, ba kuwa zan taɓa rabuwa da su ba.”
14 Haka fa Sulemanu ya gama gina Haikali.
15 Ya yi bango na ciki da katakan itacen al'ul tun daga ƙasa har sama, ya kuma rufe daɓen da itacen fir.
16 Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi can ƙuryar Haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne , an manne masa katakan itacen al'ul tun daga ƙasa har sama.
17 Tsawon sauran Wuri Mafi Tsarki kuwa kamu arba'in ne.
18 Katakan itacen al'ul na cikin Haikalin, an yi musu zāne mai fasalin gora da na furanni buɗaɗɗu. An rufe bangon daga ciki duka da itacen al'ul, har ba a ganin duwatsun ginin.
19 Ya shirya Wuri Mafi Tsarki na can cikin Haikalin domin a ajiye akwatin alkawari na Ubangiji.