9 Ta haka ya gina Haikalin, ya rufe shi da katakan itacen al'ul.
10 Benayen da ya gina kewaye da Haikalin, kowane bene tsayinsa kamu biyar. An haɗa su da Haikalin da katakan itacen al'ul.
11 Ubangiji ya ce wa Sulemanu,
12 “Idan ka yi biyayya da dokokina da umarnaina, to, zan cika maka alkawarin da na yi wa tsohonka Dawuda.
13 Zan zauna tare da mutanena, wato Isra'ila, a wannan Haikali da kake ginawa, ba kuwa zan taɓa rabuwa da su ba.”
14 Haka fa Sulemanu ya gama gina Haikali.
15 Ya yi bango na ciki da katakan itacen al'ul tun daga ƙasa har sama, ya kuma rufe daɓen da itacen fir.