2 Ya kuma gina wani ɗaki da katakai daga kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, faɗinsa kuma kamu hamsin, tsayinsa kuwa kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al'ul. Aka shimfiɗa katakan itacen al'ul a bisa ginshiƙan.
3 Aka rufe shi da katakan al'ul a bisa ɗakuna arba'in da biyar da suke gefe, waɗanda suke bisa ginshiƙai. Ɗakuna goma sha biyar a kowane jeri har jeri uku.
4 Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana daura da 'yar'uwarta, har jeri uku.
5 Dukan ƙofofin da madogaransu murabba'i ne, taga kuma tana daura da 'yar'uwarta har jeri uku.
6 Ya yi babban shirayi mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, faɗinsa kamu talatin. Akwai kuma wani shirayi mai ginshiƙai a gabansa.
7 Ya kuma gina shirayi ta sarauta inda zai riƙa yin shari'a, ya rufe dukan daɓenta da itacen al'ul.
8 Ya gina gidan da zai zauna a farfajiya na ciki, wajen shirayi. ya kuma gina wa matarsa, 'yar Fir'auna, gida irin wannan.