1 Sar 7:40-45-51 HAU

40-45 Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe da manyan cokula, da daruna. Haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sulemanu a cikin Haikalin Ubangiji. Ga abin da ya yi.ginshiƙai biyudajiya da take a kawunan ginshiƙanraga biyu don rufe dajiyar da take akawunan ginshiƙaisiffofin rumman ɗari huɗu dominraga biyu ɗin, da jeri biyu nasiffofin rumman domin kowaceraga don a rufe dajiyar da take akawunan ginshiƙandakalai gomadaruna goma a kan dakalankwatarniya ɗayasiffofin bijimai guda goma sha biyuda kwatarniya take zaune a kai,tukwanen ƙarfe, da manyan cokula,da kwanoniDukan kayayyakin aiki a cikin Haikalin Ubangiji waɗanda Huram ya yi wa sarki Sulemanu, an yi su ne da gogaggiyar tagulla.

46 Sarki ya sa a yi zubinsu a filin Urdun a ƙasar yumɓun da yake tsakanin Sukkot da Zaretan.

47 Sulemanu bai auna nauyin kayayyakin aikin ba domin sun cika yawa. Ba a kuma san nauyin tagullar ba.

48-50 Sulemanu ya yi dukan kayayyakin aikin da suke na Haikalin Ubangiji.bagaden zinariyateburin zinariya inda ake ajiyegurasar ajiyewaalkuki na zinariya guda biyar a gefendama, biyar kuma a gefen hagu agaban Wuri Mafi Tsarki na cancikifurannifitiluarautakifinjalai na zinariyahantsukadarunacokulafarantan wuta na zinariya tsantsaalmanani na zinariya domin ƙofofinɗaki na can cikin Haikali, watoWuri Mafi Tsarki, da ƙofofinHaikalin

51 Haka sarki Sulemanu ya gama dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sai ya kawo abubuwan da tsohonsa Dawuda ya keɓe, wato azurfa, da zinariya, da kayayyakin aiki, ya ajiye su cikin taskokin Haikalin Ubangiji.