3 Dukan dattawan Isra'ila suka zo, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin,
4 suka kawo tare da alfarwa ta sujada, da dukan tsarkakan tasoshin da suke cikin alfarwar. Firistoci da Lawiyawa suka kawo su.
5 Sarki Sulemanu kuwa tare da dukan taron jama'ar Isra'ila, waɗanda suka taru a gabansa, suna tare a gaban akwatin alkawari, suna ta miƙa sadakoki, da tumaki, da bijimai masu yawa, har ba su ƙidayuwa.
6 Sa'an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji suka sa a cikin Wuri Mai Tsarki na can ciki a Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi.
7 Gama fikafikan kerubobin suna buɗe a bisa wurin da akwatin alkawarin yake domin su rufe akwatin alkawarin da sandunansa.
8 Sandunansa suna da tsawo har ana iya ganinsu daga ɗaki na can ciki daga Wuri Mai Tsarki, amma ba a iya ganinsu daga waje. Suna nan haka har wa yau.
9 Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da jama'ar Isra'ila sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar.